Aiki sai mai shi: Yadda Ɗansanda yayi kwantan ɓauna a cikin lamba 2 yana dakon wani ɗan fashi (HOTO)

Aiki sai mai shi: Yadda Ɗansanda yayi kwantan ɓauna a cikin lamba 2 yana dakon wani ɗan fashi (HOTO)

- Ruwa ya kare ma wani dan gawurtaccen dan fashi a garin Fatakwal

- Dan fashin ya gamu da ajalinsa ne a hannun wani kwararrren dansanda

Kwanan wani dan fashi daya addabi al’ummar jihar Ribas sun kare bayan da ya fita tare da abokan aikinsa don yin sana’ar tasu ta Da’u fataken dare, masu barci da rana.

NAIJ.com ta ruwaito wannan lamari ya auku ne a ranar Talata 4 ga watan Yuli a unguwar Mgbuosimiri na garin Fatakwal, inda dan fashin ya tsere bayan da jami’an Yansanda suka biyo shi.

KU KARANTA: Masu gudu: EFCC tayi carafken cafke tsohon gwamnan jihar Jigawa a Abuja

Sai dai abinka da ajali, musamman idan ta hadu da kwarewa da sanin makaman aiki, ashe akwai wani dansanda da yayi bakam a cikin kwata yana dakon isowar dan fashin.

Aiki sai mai shi: Yadda Ɗansanda yayi kwantan ɓauna a cikin lamba 2 yana dakon wani ɗan fashi (HOTO)

Dansandan

Da isarsa daidai kan titin Oroazi inda dansandan yayi kwnatan bauna cikin wata kwata, bai yi wata wata ba, ya dirka ma dan fashin harsashi, nan ya fadi matacce har lahira.

Aiki sai mai shi: Yadda Ɗansanda yayi kwantan ɓauna a cikin lamba 2 yana dakon wani ɗan fashi (HOTO)

gawra dan fashin

A gaskiya wannan jami'in dansanda ya cancanci yabo:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda yan kungiyar asiri suka kashe yaron makauniya, Kalli:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel