Naira tayi irin tashin da ba ta taba yi ba cikin tsawon lokaci

Naira tayi irin tashin da ba ta taba yi ba cikin tsawon lokaci

– Darajar Naira tayi wani irin mugun karuwa

– Yanzu haka dai Naira ta kai kasa da N359

– Dama CBN ya kara sakin Dalolin Miliyoyi

Jiya kun ji cewa ana sa ran cewa Naira za ta kara daraja a kasuwa kuma hakan ya faru. Yanzu haka Naira tayi wani mugun tashi a kasuwar canji inda ta kai har kasa da N360.

Naira tayi irin tashin da ba ta taba yi ba cikin tsawon lokaci

Madalla: Darajar Naira ya babbako Hoto daga yanar gizo

A karshen makon can ne Dala ta kai N365 bayan da ta na kan N366. To yanzu haka ma dai Dalar ta kara yin kasa zuwa N359. An dai dade Dala ba tayi irin wannan sauka ba har na kusan N6 kamar yadda mu ka samu rahoto.

KU KARANTA: Wani ya hadiye kusan Biliyan guda a ciki

Naira tayi irin tashin da ba ta taba yi ba cikin tsawon lokaci

Tattalin arziki: Naira ta kara daraja a kasuwa

Dama wani Jami’in Babban Bankin kasar CBN Isaac Okarafor ya bayyana cewa CBN zai saki fiye da Dala Miliyan 100. Hakan ne dai ke sa a samu saukin Dalar a kasuwa. An dai saki wasu makudan Miliyoyin ga kuma wasu ‘Yan kasuwar.

Ko a karshen wancan Watan dai babban bankin kasar ya saki wasu Dala Miliyan 195 domin a samu sa’ida wajen harkar Dalar Amurkar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ina Shugaba Buhari Inji 'Yan Najeriya [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel