Gwamna Al-Makura ya nemi a soke Majalisar Dattawa ko ta Tarayya

Gwamna Al-Makura ya nemi a soke Majalisar Dattawa ko ta Tarayya

– Gwamnan Jihar Nasarawa ya nemi a soke Majalisun Najeriya

– Al-Makura yace babu dalili a cigaba da aiki da Majalisu biyu

– Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da aka kai masa ziyara

Gwamnan Jihar Nasarwa Umaru Tanko Al-Makura yayi kira a soke daya daga cikin Majalisun Tarayya don kuwa babu dalilin a cigaba da aiki da dukka biyu ba Inji Gwamnan.

Wani Gwamna ya nemi a soke Majalisar Dattawa ko ta Tarayya

Hoton Gwamnan Nasarawa a Majalisa

Umaru Tanko Al-Makura yake cewa idan ‘Yan kasar sun zabi su bi Majalisar Dattawa to sai a soke Majalisar Wakilai haka kuma idan Majalisar Wakilan aka zaba. Najeriya na kashe kudi makuku wajen albashin ‘Yan Majalisar.

KU KARANTA: Sanatoci sun yi kokarin tunbuke Osinbajo?

Wani Gwamna ya nemi a soke Majalisar Dattawa ko ta Tarayya

Hoton Gwamna Al-Makura a wajen zabe

Al-Makura ya bayyana hakan ne a lokacin da Shugaban tsofaffin Daliban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya watau Farfesa Ahmed Tijjani M. Gwamnan ya kuma bayyana cewa babu dalilin kara Jihohi a kasar. Gwamnan a karshe yayi kira a fahimci tsarin kasar da kyau.

Kun ji cewa daga fitar Osinbajo wajen Najeriya Sanatoci sun yi kokarin nada Saraki Shugaban kasa na rikon kwarya jiya. Wasu Sanatoci ne su ka kawo wannan kuduri sai dai tuni Saraki yayi watsi da maganar.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko 'Yan kasar nan su gaji da Shugaba Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel