Inyamurai: Ango Abdullahi ya gamu da suka daga wani Farfesa

Inyamurai: Ango Abdullahi ya gamu da suka daga wani Farfesa

– Farfesa Jerry Ghana yayi kaca-kaca da Dattijon Arewa Ango Abdullahi

– Tsohon Ministan yace Farfesa Ango ya shi kunya kwarai da gaske

– Jerry Ghana yayi wannan bayani ne a wani coci da ke Maitama a Abuja

Tsohon Ministan nan Farfesa Jerry Ghana ya dura kan Ango Abdullahi. Jerry Ghana yace ya ji dadi da ba Ango Abdullahi ne Shugaban sa a Jami’a ba. Farfesa Ghana yayi karatu ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.

Inyamurai: Ango Abdullahi ya gamu da suka daga wani Farfesa

Hotunan Ango Abdullahi daga NAIJ.com

Farfesa Jerry Ghana da yake magana game da raba Najeriya kamar yadda ku ka ji a wani coci ya soki Dattijon nan na Farfesa Ango Abdullahi kan matsayar sa game da Inyamurai. Ango Abdullahi ya marawa wasu Matasa baya bayan sun yi kira ga Inyamurai su bar Yankin kasar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi magana dame da Marigayi Dan masani

Ghana yayi Allah-wadai da wannan matsaya na Dattijon, yace abin kunya ne kwarai irin sa yayi wannan aiki. Har ta kai Jerry Ghana yace ya ji dadi da ba Ango Abdullahi ya sa hannu a shaidar takardar Digirin sa ba domin ba shi bane Shugaban Jami’a lokacin da yayi karatu ba.

Dazu ai kun ji cewa tsohon Ministan yada labarai na Najeriya Farfesa Jerry Ghana yace idan fa aka tashi raba kasar nan to su fa ba ‘Yan Arewa ba ne. Farfesan yace babu dalilin da zai sa su tsaya tare da sauran ‘Yan Arewa.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ta kama 'Yan Najeriya su mutu don Buhari ya rayu za su yi? [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel