Majalisar Dattawa ta yi yunkurin bayyana Saraki a matsayin mukaddashin shugaban kasa

Majalisar Dattawa ta yi yunkurin bayyana Saraki a matsayin mukaddashin shugaban kasa

- ‘Yan majalisar dattawa sun yi yunkurin kafa Saraki a matsayin mukaddashin shugaban kasa

- Sanata Kabiru Marafa ya ce shugaban majalisar ya kamata ya zama mukaddashin shugaban kasa yanzu tun da Osinbajo ba ya nan

- Yau ne majalisar dattijai ta dawo daga hutun makonni 3

A zaman ta na yau Talata, 4 ga watan Yuli majalisar dattijan Najeriya ta yi yunkurin bayyana shugaban majalisar dattawan, sanata Abubakar Bukola Saraki a matsayin mukaddashin shugaban kasar.

Majalisar dattijai bayan dawowar ta daga hutun makonni uku ta samu wata wasika daga mukaddashin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo inda yake bukatar a tabbatar da Mista Lanre Gbajabiamila a matsayin babban darakta na National Lottery Regulatory Commission.

Sanata Eyinanya Abaribe mai wakiltar mazabar Abia ta Kudu yayin da yake magana ya ce babu wanda ke kasar nan yanzu haka da shugaban kasar Muhammadu Buhari da kuma Farfesa Yemi Osinbajo.

Majalisar Dattawa ta yi yunkurin bayyana Saraki a matsayin mukaddashin shugaban kasa

Sauren majalisar dattijan Najeriya Source: @NGRSenate

KU KARANTA: Majalisar dattijai ta sha alwashin sanya kafar wando daya da fadar Shugaban Kasa

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, ‘yan majalisar sun amince da maganar sanata Eyinanya Abaribe. Sanata Kabiru Marafa mai wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya ya ce idan shugaban kasa ba ya nan, mataimakin shugaban kasar zai ci gaba da shugabanci, kuma idan mataimakin shugaban kasar ne ba ya nan, shugaban majalisar dattawa ya kamata ya zama mukaddashin shugaban kasa tun da shine na uku a jerin shugabancin kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel