Jerin mutanen da su ka halarci Sallar Jana’izar Marigayi Dan Masanin Kano

Jerin mutanen da su ka halarci Sallar Jana’izar Marigayi Dan Masanin Kano

- Gwamnan Kano ya jagoranci jama’a wajen birne Marigayi Maitama Sule

- Shugaban Majalisa Bukola Saraki yana cikin wadanda suka halarci sallar

- Sauran manyan Gwamnoni da mutanen Kasa sun yi Dattijon Sallah

A jiya ne Dan Masanin Kano ya cika a wani Asibitin kasar Masar. Manyan Kasa dai sun halarci sallar da aka yi masa. Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Ganduje ya jagoranci jama’a wajen birne tsohon Ministan.

Jerin mutanen da su ka halarci Sallar Jana’izar Marigayi Dan Masanin Kano

Hotunan mutanen su ka halarci Jana’izar Maitamadaga Gwamnatin Kano

Sauran Gwamnonin Jihohin Jigawa, Bauchi da Sokoto, dsr sun halarci sallar. Haka kuma Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki yana cikin wadanda suka halarci sallar. Sauran Ministocin kasar irin su Hadi Sirika da Kayode Fayemi sun halarci Jana’izar.

KU KARANTA: Sanatoci za su kafa wando daya da Buhari

Jerin mutanen da su ka halarci Sallar Jana’izar Marigayi Dan Masanin Kano

Bukola Saraki wajen sallar jana'izar Dan masani daga Gwamnatin Jihar Kano

Gwamnatin Tarayya ta aiko wakilai karkashin Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnati Abba Kyari. A jiya Shugaba Buhari ya aiko takarda ta musamman inda yake takaicin rashin Maitama Yusuf yace an yi rashi.

Jerin mutanen da su ka halarci Sallar Jana’izar Marigayi Dan Masanin Kano

An bizne ‘Dan Masanin Kano dazu. Hoto: Salihu Tanko Yakassai Dawisu

Babban Jigo a Jam’iyyar APC Bola Tinubu yace ba shakka an rasa wadanda su ka rage cikin iyayen kasar da ake da su. Dan Masanin Kano mutum ne mai baiwar magana kuma mai son kasar nan da gaskiya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel