Buhari zai iya mulkin Najeriya ko a keken Guragu yake – Tsohon Soja

Buhari zai iya mulkin Najeriya ko a keken Guragu yake – Tsohon Soja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai iya mulkan Najeriya ko da akan keken Guragu yake zama ko yana rike da sandan Guragu ne, inji wani sahibin shugaba Buhari, Kyaftin Joseph Din.

Daily Trust ta ruwaito Kyaftin Din yana bayyana haka ne a yayin bikin cikarsa shekaru 80 daya gudana a gidansa dake garin Jos, inda yace shugaba Buhari ne kadai zai iya kai kasar nan zuwa gaci.

KU KARANTA: Tuna baya: Kalli hotunan Maitama Sule yayin dayake ganiyar ƙuruciyarsa

Dayake mayar da martani game da maganan da gwamnan jihar Ekiti Fayose yake yi, Din ya bukaci yan Najeriya dasu manta da gwamnan, wanda yace yana neman suna ne kawai, inji majiyar NAIJ.com.

Buhari zai iya mulkin Najeriya ko a keken Guragu yake – Tsohon Soja

Buhari

“Menene matsalar Fayose? Me yasa yake magana akan lafiya Buhari bayan shi ba likita bane. Don haka nake shawartar yan Najeriya da suyi watsi da shi, don kuwa Buhari zai iya mulkin kasar nan koda kuwa a keken guragu yake zama.” Inji Din.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wai ina Baba Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel