Masu gudu: EFCC tayi carafken cafke tsohon gwamnan jihar Jigawa a Abuja

Masu gudu: EFCC tayi carafken cafke tsohon gwamnan jihar Jigawa a Abuja

- EFCC ta samu nasarar kama gwamnan jigawa da take nema ruwa a jallo

- Saminu Turaki ya shiga hannu ne yayin halartan wani taro a Abuja

Hukumar yaki da almundahana dayi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta cika hannu da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Saminu Turaki.

EFCC tayi ram da Saminu ne sakamakon zarginsa da wawusan dukiyar jihar, tare da yi ma baitul malin jiha karkaf, a zamanin da yayi mulkin jihar, daga 1999-2007.

KU KARANTA: Tuna baya: Kalli hotunan Maitama Sule yayin dayake ganiyar ƙuruciyarsa

NAIJ.com ta ruwairo jami’an hukumar EFCC sunyi diran mikiya ne a yayin wani taron kaddamar da littafin tarihin marigayi Birgediya Zakari Mai Malari a Abuja, a nan ta cika hannu da tsohon gwamnan

Masu gudu: EFCC tayi carafken cafke tsohon gwamnan jihar Jigawa a Abuja

Saminu Turaki

Tun a shekarar 2011 ne EFCC ta ke neman Saminu Turaki ruwa a jallo, biyo bayan umarnin mai shari’a Yahuza na babban kotun tarayya dake Dutse, sakamakon tuhumarsa da take yi kan aikata laifuka 36 da suka shafi almundahana da wawuran kudi.

Ko a shekarar 2016, a ranar 19 ga watan Mayu, sai da EFCC ta kai samame gidan Saminu dake Unguwar Asokoro bayan samun tsegumi daga wata majiya mai karfi, amma koda suka iso gidan, sai ya tsere.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idana an so in yi sata, sai in yi, Inji wani mutum, Kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel