HOTUNAN yayinda gawar Danmasanin Kano ta isa jihar Kano

HOTUNAN yayinda gawar Danmasanin Kano ta isa jihar Kano

- Gawar Danmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule ya isa jihar Kano

- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje tare da sauran manyan gwamnati ne suka tarbi gawar

- An karbi gawar Marigayin a sansanin jiragen sojojin sama dake Kano

Rahotanni sun kawo cewa gawar Danmasaini Kano kuma tsohon ministan Najeriya, Alhaji Yusuf Maitama Sule ya isa jihar Kano.

A dazu ne Legit.ng ta samu labarin isar gawar Danmasanin Kano da ya rasu a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli a kasar Masar babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban ma’aikata na tarayya, Abba Kyari, ne ya karbi gawar a ranar Talata, 4 ga watan Yuli tare da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana’izar Danmasanin Kano.

KU KARANTA KUMA: Za’ayi jana’izar Danmasanin Kano a yau Talata da Misalin Karfe hudu

Jirgin dake dauke da gawar ya iso da misalin karfe 1:54 na rana.

A yanzu dai gwamnan jihar Kano, Alhaji Umar Ganduje, tare da manyan jami'an gwamnatin tarayya da kuma na jiha suka karbi gawar Marigayin a sansanin jiragen sojojin sama dake Kano.

Ga hotunan a kasa:

HOTUNAN yayinda gawar Danmasanin Kano ta isa jihar Kano
HOTUNAN yayinda gawar Danmasanin Kano ta isa jihar Kano Hoto: daga shafin Rariya

HOTUNAN yayinda gawar Danmasanin Kano ta isa jihar Kano
Manyan masu fada sun taru don karban gawar Hoto: daga shafin Rariya

HOTUNAN yayinda gawar Danmasanin Kano ta isa jihar Kano
An karbi gawar Marigayin a sansanin jiragen sojojin sama dake Kano Hoto: daga shafin Rariya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel