Labari da dumi-duminsa: An wanke Ali Ndume daga zargin alaka da Boko Haram

Labari da dumi-duminsa: An wanke Ali Ndume daga zargin alaka da Boko Haram

- Shekaru biyar bayan fara shari'ar, an wanke Ali Ndume

- Anyi zargi da karar Ali Ndume kan alaka da Boko Haram

- Duk da ana shari'ar, Ali Ndume ya sake cin zaben sanata

An tuhumi Ali Ndume kan zargin kin bayar da bayanai kan Boko Haram, bayan yana da bayanan sirrin nasu, zargin da ya musanta, inda ya ce tsohon mataimkin shugaba Jonathan na karbar bayanan sa na sirri kan Boko Haram.

A yanzu ne dai wata babbar kotu a Abuja ta wanke Sanata Ali Ndume daga dukkan zarge zarge da ake yi masa kan ta'addanci, boye bayanai, da ma daukar nauyin Boko Haram da kudinsa, shari'ar da ya shekara biyar yana fuskanta.

Labari da dumi-duminsa: An wanke Ali Ndume daga zargin alaka da Boko Haram

Labari da dumi-duminsa: An wanke Ali Ndume daga zargin alaka da Boko Haram

An dai sami lambobin wayar wasu 'yan Boko Haram ne a wayar salular Sanatan, inda yace ya samu ne lokacin da yake kokarin ganin anyi sulhu da gwamnati domin a kauce wa yaki a yankin na Borno, a lokacin yana cikin kwamitin sulhu da shugaba Jonathan ya kafa.

KU KARANTA KUMA: Gawar Marigayi Maitama Sule ta Iso Abuja

A cewar lauyansa, Rickey Tarfa, dama babu wani kes kan Ali Ndume, domin haka babu wata shari'a a kansa, batu da alkali Jastis, Kolawale ya karba, ya wanke Sanatan tsaf da sabulu.

A yanzu dai Sanatan ya sami 'yanci duk da cewa shari'ar ta dade, ta bata masa suna, kuma ta jawo masa yawan kyama tsakanin 'yan Najeriya.

Ku boyo mu a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel