Maharan Boko Haram sun yi garkuwa da mata da yara a ƙasar Nijar

Maharan Boko Haram sun yi garkuwa da mata da yara a ƙasar Nijar

- Yan Boko Haram sun kai hari a kasar jamhuriyyar Nijar

- Yan Boko Haram sun sace mata da kananan yara 40

Wasu rahotanni daga kasar jamhuriyar Nijar sun bayyana cewar mayakan Boko Haram sun kai hari kasar Nijar inda suka kashe mutane 9 tare da sace mata kimanin 40.

Harin ya wakana ne a daren Lahadi 2 ga watan Yuli a wani kauyen Ngalewa dake kan iyakar kasar Nijar da Najeriya, kamar yadda rediyon BBC Hausa suka ruwaito.

KU KARANTA: Maganganu 10 masu ɗauke da darussa daga bakin sarkin Magana, Maitama Sule

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wani mutumi mai suna Mamman Nour yana fadin “Mutum 9 aka kashe, tare da sace mata akalla su 30.”

Maharan Boko Haram sun yi garkuwa da mata da yara a ƙasar Nijar

Sojoji a Nijar

Shima magajin garin, Abba Gata Issa ya tabbatar da faruwar lamarin. haka zalika a satin data gabata, an kai harin kunar bakin wake a wata sansanin yan gudun hijira inda mutane 2 suka mutu, 11 suka jikkata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kuna ganin yan Najeriya sun gaji da Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel