Za’ayi jana’izar Danmasanin Kano a yau Talata da Misalin Karfe hudu

Za’ayi jana’izar Danmasanin Kano a yau Talata da Misalin Karfe hudu

- Za’ayi jana’izar Danmasanin Kano, Alhaji Maitama Sule a yau Talata

- Alhaji Maitama Sule ya rasu ya bar 'ya'ya 10

- Ya rasu ne inda ya je jinya a wata asibiti dake Al-Qahira a kasar misira a jiya 3 ga watan Yuli

Za’ayi jana’izar Danmasanin Kano, Yusuf Maitama Sule a yau Talata, 4 ga watan Yuli da misalin karfe hudu.

Babban dan marigayin, Alhaji Mukhtari Maitama, ya bayyana cewa a ranar Asabar da ta gabata ne Alhaji Yusuf Maitama Sule ya bar gida Najeriya zuwa al-Qahira a kasar Misra don jinya.

Alhaji Maitama Sule ya rasu ya bar 'ya'ya 10 da kuma matar aure guda daya.

Za’ayi jana’izar Danmasanin Kano a yau Talata da Misalin Karfe hudu

Za’ayi jana’izar Danmasanin Kano a yau Talata da Misalin Karfe hudu

A yayinda ya isa kasar Misra anyi masa wasu gwaje-gwaje inda suka gano cewa yana dauke da wasu lalura amma kafin basa wani taimako rai yayi halinsa a safiyar jiya, Litinin 3 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Maganganu 10 masu ɗauke da darussa daga bakin sarkin Magana, Maitama Sule

Maitama Sule ya kasance jarumi, mai juriya da hakuri. Yana kuma girmama kowa. Ya nuna wa 'ya'yansa kada su raina kowa ko tsangwamar kowa. Yadda yake karbar mutane haka yake cudanya da 'ya'yansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin zaka taimaka ma Buhari ya samu waraka daga cutar dake damunsa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel