Zamu iya ma shugaba Buhari magani - Kungiyar masu maganin gargajiya

Zamu iya ma shugaba Buhari magani - Kungiyar masu maganin gargajiya

-Muna kishin shugaba Buhari kuma munyi imanin zamu iya masa magani idan an neme mu.

-Yan Najeriya da yawa suna rasa rayukan su domin suna kyaman magungunan gargajiya.

-Tsohon Shugaba Obasanjo yana nan garau domin yana amfani da magungunan gargajiya.

Hadadiyar kungiyan masu magungunan gargajiya na kasa (NANTMP) tayi ikirarin cewa yan kungiyan za su iya ma Shugaba Buhari magani idan da za'a basu daman yin hakan.

Uban kungiyan Dr. Adesunmiboye Fawawo ya bayyana hakan ne a ranar Talata a garin Oshogbo a wajen taron zaben sababin shugabanin kungiyan.

Yace yan Najeriya da yawa suna rasa rayyukan su saboda suna kyaman magungunan mu na gargajiya wanda galibi daga itatuwa muke yi, sun gwammace suyi amfani da magungunan zamani na bature.

'Zamu iya ma shugaba Buhari magani' - Kungiyan masu maganin gargajiya.

'Zamu iya ma shugaba Buhari magani' - Kungiyan masu maganin gargajiya.

Ya kara da cewa "Muna kishin shugaba Buhari domin shugaban kasar mu ne, kungiyar mu tana da rajista kuma ta samu amincewan gwamnatin tarayya. An kafa kungiyan ne a zamanin gwamnatin Obasanjo, kuma yana amfani da magungunan mu wanda yanzu garau yake duk da yawan shekarun sa.

KUMA KU KARANTA: Hadimar Buhari ta mayar wa da Fayose Martani

Ya kara da cewa "Muna kishin shugaba Buhari domin shugaban kasar mu ne, kungiyar mu tana da rajista kuma ta samu amincewan gwamnatin tarayya. An kafa kungiyan ne a zamanin gwamnatin Obasanjo, kuma yana amfani da magungunan mu wanda yanzu garau yake duk da yawan shekarun sa.

"Mun warkar da marasa lafiyan da yan uwansu sun cire rai akan su, abin takaici babu wanda ya nemi mu akan rashin lafiyar shugaba Buhari. Babu bukatar shugaba Buhari ya tafi kasan waje, zamu iya masa magani a gida Najeriya.

"Akwai gawawakin mutane masu arziki sosai a asibitocin Najeriya domin sun ki amafani da magungunan gargajiya. Amfani da magungunan bature masu tsada yana kara jefa tatalin arzikin kasar mu cikin tsaka mai wuya".

Fawowo ya cigaba da cewa, mafi yawan mutanen da ke kushe maganin mu suna cewa maganin zai iya kawo ciwon koda wanda ba gaskiya bane, domin muna kayyade addadin maganin da za'a sha.

Kamar yadda ya bayyana, muna fitar da magungunan gargajiya zuwa kasashen waje kuma akwai wasu asibitocin mu na gida Najeriya da ke amfani da magungunan namu kamar 'seleru agbo' wanda yace ana amfani dashi a asibitin koyawar na jami'ar Akintola da ke garin Oshogbo.

Sakataren kungiyar, Dr Ade Adeagbo ya koka da yadda mutane ke kashe kudi mai yawa wajen siyo magungunan bature amma suna gudun magugunan gargajiya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel