Wani dan Najeriya a Turai ya hadiye kwatankwacin naira biliyan daya a cikinsa

Wani dan Najeriya a Turai ya hadiye kwatankwacin naira biliyan daya a cikinsa

- 'Yan Najeriya a Turai sunyi kaurin suna wajen aikata muggan laifuka a duniya

- Wani dan Najeriya ya lakume kudi a cikin kwaroron roba

- Kudaden kasar wajen makudai in ka kwatanta su da Naira

A gabashin kasar Faransa a Turai, an damke wani dan Najeriya bayan da ya hadiyi kudin Yuro kusan dubu tamanin ($80,000), a cikinsa.

An sami wadannan kudade ne an cusa su a kwaroron roba na kwandan, anyi jerinsu an hadiye. Wasu daga kudin kuma wadanda basu sami shiga robar ba, sai ya sanya su cikin kayansa ya boye.

Wani dan Najeriya a Turai ya hadiye kwatankwacin naira biliyan daya a cikinsa

Wani dan Najeriya a Turai ya hadiye kwatankwacin naira biliyan daya a cikinsa

Wannan abin mamaki dai ya faru ne a Birnin Strasburg na gabashin kasar Faransa, karnukan jami'an kwastan ne dai suka tona shi, bayan sunji warin tabar wiwi da ya makaro a kayansa da niyyar safararsu.

Da dai aka ga mutumin na zazzare idanu, sai aka saka shi a na'urar mayatar bature, mai gani har hanji, wato X-Ray machine, inda aka gano jerin kudaden a shirye a cikin kwaroron roba a hanjinsa.

KU KARANTA KUMA: An zargi Buhari da raba kan 'yan Najeriya

Yawan kudin dai da aka kama sun kai kusan Naira biliyan daya, wadanda mai yawansu, a tumbin wannan tahaliki aka same su. An kuma yi sa'ar bashi magani domin ya amayo su, amma ba'a sami sa'ar hakan ba, sai dai kashinsu da yayi.

An garzaya da wannan ja'iri kotu inda aka tuhume shi da fasa kwabrin kudi da kwayoyi, da ma yiwa jami'an kwastan karya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel