Kakakin Majalisar Wakilai na alhinin jibge sojoji a jihohi 28 na kasar nan

Kakakin Majalisar Wakilai na alhinin jibge sojoji a jihohi 28 na kasar nan

- Dogara ya ce aikin soji daban na yansanda daban

- A yanzu dai kamar muna cikin zaman ko-ta-kwana ne

- An girke soji a johohi daban daban kan batun tsaro

A taron da ake yi a cikin majalisa, shugaban majalisar wakilai ya nuna rashin gamsuwarsa da yadda a yanzu saboda dalilai na tsaro, ake girke sojoji da dama a jihohin Najeriya, wanda a cewarsa, ba haka ya kamata a gani ba a lokutan zaman lafiya.

Kakakin Majalisar Wakilai na mamakin jibge sojoji a jihohi 28 na kasar nan

Kakakin Majalisar Wakilai na mamakin jibge sojoji a jihohi 28 na kasar nan

A zaman da ake yi a zauren majalisar don taron kwamitin tsaro na majalisar, inda yace 'abin tsoro ne a ce a lokacin mulkin farar hula, kuma ana zaman lafiya, ace sojoji su ne ke tabbatar da zaman laifya a johohin kasar nan.'

KU KARANTA KUMA: Idan Najeriya ta balle tsere wa zamuyi, wani dattijon Arewa

Kakaki Dogara, ya sha alwashin fitar da kudaden tsaro ga hukumomin tsaro ke bukatar su domin tabbatar da zaman lafiyar kasa.

A cewarsa dai, jihohin da soji ke zaman tsaro sun kai 28, a rigingimu da suka sha kan 'yansanda, wadanda alhakinsu ne tabbatar da tsaro.

A yanzu dai jihohi irinsu Borno, Adamawa, Yobe, Delta, Plateau, Taraba, da Bayelsa, duk sojoji ke aikin tsaro a kasar nan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel