Dangon Tsuntsaye sun tilasta wa jirgin sama sauko wa kasa

Dangon Tsuntsaye sun tilasta wa jirgin sama sauko wa kasa

- An samu tsuntsaye guda biyu a titin jirgin sama

- Matukan jirgi sunyi saukar gagawa bayan jirgin ya fara jijiga da kara

- A makon da ya wuce, wani jirgin ya fuskanci matsala irin wannan.

Wasu tsuntsaye sun sa wani jirgin saman AirAsia X saukan gagawa. Shi dai jirgin asali yana hanya zuwa birnin Kwala Lumpur ne na kasar Malaysia amma ya yada zango a kasar Australia.

Fasinjojin cikin jirgon wanda yawan su ya kai 359 sun firgita ne bayan jirgin ya tashi daga garin Gold Coast da ke Australia.

Kafin saukan jirgin, an ruwaito cewa an rika jin tartatsin wuta daga injin jirgin.

Dangon Tsuntsaye sun tilasta wa jirgin sama sauko wa kasa - daga shafin bbc hausa

Dangon Tsuntsaye sun tilasta wa jirgin sama sauko wa kasa - Hoto daga shafin bbc hausa

KUMA KU KURANTA: 'Gwamnatin Buhari ta raba kan mutanen Nigeria' - Tsofafin ministocin PDP

Kamfanin jirgin yace "An samu wasu tsuntsaye guda biyu a titin jirgin"

Wani fasinja da ke cikin jirgin yace "Na ji kara kamar sau uku zuwa biyar kafin naga wuta daga waje"

Ya kara da cewa "Daga nan sai naji jirgin yana girgiza, sai kuma muka ji wata kara mai karfi." Kamar yada ya bayyana wa kafar yadda labarai na Sydney Morning Herald.

Wani fasinja mai suna Eric Lim shima ya bada labarin faruwan al'amarin ta shafinsa na facebook kamar haka. "Kara muka ji iri-iri a yayin da su kuma fasinjojin jirgin suka rika kwantsama ihu"

Shugaban Kamfanin jirgin Benyamin Ismail yace an tanadi wani jirgin da zai kwashe fasinjojin zuwa birnin Kwala Lumpur.

Ko a makon da ya gabata, an sami faruwan wani al'amarin da yayi kama da wannan inda jirgin ya rika jijiga kuma ya tilasta ma matukan jirgin saukar gagawa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel