Majalisar dattijai ta sha alwashin sanya kafar wando daya da fadar Shugaban Kasa

Majalisar dattijai ta sha alwashin sanya kafar wando daya da fadar Shugaban Kasa

- Majalisar dattawan Najeriya ta yi barazanar sanya kafar wando daya da fadar shugaban kasa kan Magu

- Majalisar ta kuma yi barazana ga mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo kan zabar Magu

A zamanta na yau Talata, 4 ga watan Yuli majalisar dattawan Najeriya ta yi kira da a dakatar da duk wata bukata ta tantance ko tabbatar da nade-naden da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo gaban ta.

Hakan ta faru ne sakamakon wani furuci da mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi na cewa wai, nade-naden mukamai na bangaren zartarwa ba sa bukatar sahalewar majalisar kasa kamar yadda sashe na 171 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Majalisar ta rikice da hatsaniya ne bayan da shugaban majalisar dattawan, Sanata Bukola Saraki ya gama karanta wasikar da mukaddashin shugaba Yemi Osinbajo ya aikewa majalisar na bukatar sahalewar majalisar don a tabbatar da Mista Lanra Gbajabiamila a matsayin shugaban hukumar wasannin caca.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Gawar Maitama Sule ya iso Abuja

Yan majalisa sunyi Allah wadai da kalaman Osinbajo, sannan kuma sun yanke hukuncin dakatar da nade-naden mukamai na bangaren zartarwa har sai an tabbatar da mene ne hakikanin ikon majalisa game da batun nade-naden mukamai

Haka kuma, ‘yan majalisar sun bayyana cewa babu daya daga cikinsu da zai sake amsa gayyata daga hukumar EFCC

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel