WAIWAYE: Abubuwa da nake fatan gani a Najeriya kafin in bar duniya - Maitama Sule

WAIWAYE: Abubuwa da nake fatan gani a Najeriya kafin in bar duniya - Maitama Sule

Tun bayan rasuwar Alhaji Yusuf Maitama Dan Masanin Kano a ranar Litinin 3 ga watan Yuli, al’umman kasar da dama ke ta mika ta’aziyyar sa ga yan’uwa da abokan arziki.

NAIJ.com ta tattaro maku wasu daga cikin abubuwa marigayin ya ce yana burin gani a Najeriya kafin ya bar duniya.

WAIWAYE: Abubuwa da nake fatan gani a Najeriya kafin in bar duniya - Maitama Sule

Abubuwa da nake fatan gani a Najeriya kafin in bar duniya cewar Maitama Sule

Gasu kamar haka:

“Ina fatan ganin dunkulalliyar Najeriya wadda al'ummar cikinta zasu kaunaci zaman lafiya da juna.

KU KARANTA KUMA: Za’ayi jana’izar Danmasanin Kano a yau Talata da Misalin Karfe hudu

“Ina burin ganin kasar Najeriya ta zama daya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki saboda tana da dimbin arzikin na albarkatun kasa da na mutane da take da shi.

“Burina na ga al'ummar Najeriya suna mutunta juna da aiki tare duk da bambancin al'ada da addini.

“Babban burina shine ganin tsarin mulkin Dimokradiyya ya samu gindin zama a Najeriya ta yadda za ta jagoranci sauran kasashen Afrika a kan harkar siyasa.

“Daga karshe ina fatan ganin an samu adalin shugabanni wadanda babu ruwansu da satar kudaden gwamnati.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel