Miliyoyin ‘yan Najeriya zasu biya kudin asibitin buhari idan ya gaza – Rochas Okorocha

Miliyoyin ‘yan Najeriya zasu biya kudin asibitin buhari idan ya gaza – Rochas Okorocha

- Rochas Okorochas ya bayyana cewa buhari ba zai rasa kudi ba a matsayinsa na mutum mai tarin jama’a

- Shugaban gwamnonin na APC ya kara da cewa shugaban kasar ya yi sadaukarwa mai girma ga kasar

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari na birnin Landan tun ranar 7 ga watan Mayu don ci gaba da jinya

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana cewa idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza biyan kudin asibitin sa, miliyoyin yan Najeriya zasu kawo masa dauki.

A cewar rahotanni, Okorocha ya yi wannan furuci ne yayinda yake zantawa da manema labarai gurin maida martini ga zargin cewa shugaban kasar na biyan kudin tafiye-tafiyen jinyarsa da kudin masu biyan haraji.

NAIJ.com ta tattaro cewa shugaban gwamnonin APC ya ce: “Idan a yau akayi wata sanarwa kan cewa shugaba buhari baida kudin da zai yi ma kansa magani a kasar waje, ku yarda dani, sama da ‘yan Najeriya miliyan 20 zasu hada kudi don lafiyar sa.

Miliyoyin ‘yan Najeriya zasu biya kudin asibitin buhari idan ya gaza – Rochas Okorocha

Miliyoyin ‘yan Najeriya zasu biya kudin asibitin buhari idan ya gaza, cewar Rochas Okorocha

“Shugaba Buhari ba zai taba rasa kudi ba. Mutane zasu tallafa mai idan bukatar yin hakan ta taso. Mutun ne da ke sadaukarwa ga mutane. Baya rayuwa dan kansa.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Buhari ya rasu Inji wani Mawakin Najeriya

“Dole ayi ma Buhari kallon babban dan Najeriya wanda ya yi sadaukarwa da dama. Kana iya ganin haka daga iyalinsa.

“Kana iya gani daga iyalinsa, yaransa. Baya maganar dukiya. Don haka duk lokacin da yake bukatar kudi, na tabbata miliyoyin ‘yan Najeriya zasu harhada koda kuwa kwabo daya ne don lafiyarsa."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na birnin Landan tun ranar 7 ga watan Mayu, inda yake jinya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel