A yayin da ake kokarin ciyar da 'yan gudun Hijira, sun haifi jarirai 3000 a bana

A yayin da ake kokarin ciyar da 'yan gudun Hijira, sun haifi jarirai 3000 a bana

- Rikicin Boko Haram: An haifi yara 3000 a sansanin yan gudun hijira a cikin wata 6

- Hukumar SEMA tana aiki tare da ma'aikatan lafiya domin taimaka ma masu jego.

- Mun sami karuwan ma'aurata a sansanin yan gudun hijira.

Hukumar bada agajin gagawa (SEMA) na jahar Borno ta ce an haifu yara guda 3000 a sansanin yan gudun hijiran a watani shida da suke wuce.

Shugaban Hukumar, Satomi Ahmad ya bada wannan sanarwan a wata ganawa da manema labarai da yayi a garin Maiduguri.

A yayin da ake kokarin ciyar da 'yan gudun Hijira, sun haifi jarirai 3000 a bana

A yayin da ake kokarin ciyar da 'yan gudun Hijira, sun haifi jarirai 3000 a bana

Shugaban yace an kidaya haihuwan ne ta hanyar tara alkuluman haihuwa a sansanin yan gudun hijira daban-daban da ke jahar Borno daga watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekaran.

Yace alkalluma haihuwan yana nuna karuwan ma'aurata dake zaune a cikin sansanin yan gudun hijiran.

KU KARANTA KUMA: An mayar wa da Fayose kakkausan martani

Ya kara da cewa "Mun samu haihuwan jarirai guda 3000 a watanni shida da suke shude. Mun taimaka ma iyayen su da magunguna da sauran kayayakin da mai jego ke bukata."

Shugaban yace hukumar SEMA tana aiki tare da ma'aikatar kiwon lafiya na jahar domin tallafa wa mata masu ciki a cikin sansanin.

Ya kuma ce hukumar SEMA ta samar da motocin daukan marasa lafiya domin samun saukin kaisu babbar asibiti idan bukatar hakan ya tasho. Har illa yau yace hukumar ta samar da abinci masu gina jiki da kayan sawa domin amfanin jariran da iyayensu mata.

A kwanakin baya, hukumar SEMA tace sun sami haihuwan guda 13,000 a cikin shekaru hudu a sansanin yan gudun hijiran da ke jahar Bornon.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel