Ana sa rai Naira ta kara daraja a kasuwa

Ana sa rai Naira ta kara daraja a kasuwa

– Darajar Naira za ta karu kwanan nan

– Haka dai masana da ‘Yan kasuwa ke sa rai

– CBN zai kara sakin wasu Dalolin Miliyoyi

Ana sa ran cewa Naira za ta kara daraja a kasuwa. Wani babban Jami’in bankin CBN ya fadi haka. Yanzu haka bankin kasar zai saki wasu Daloli.

Ana sa rai Naira ta kara daraja a kasuwa

Hoton babban Bankin kasar na CBN

NAIJ.com na samun rahoto cewa ana sa rai darajar Naira ta karu nan ba da dadewa ba a dalilin Dalolin da Bankin kasar na CBN ke cigaba da amai a kasuwa. Mista Isaac Okarafor ya bayyana wannan.

KU KARANTA: Kwastam ta fara gwanjon motoci

Babban Bankin kasar CBN zai saki fiye da Dala Miliyan 100 domin a samu saukin Dalar a kasuwa. Tuni dai har an saki Dala Miliyan 100 ga manyan ‘Yan kasuwa. Za kuma a kara sakin wasu Dala Miliyan 50 ga masu karamin jari.

Haka kuma Bankin zai saki Dala Miliyan 45 ga masu fita kasar waje. Hakan dai zai sa Dalar tayi sauki. Ana ganin amfanin tsarin babban bankin CBN. Yanzu Naira ta dan kara daraja a kasuwa bayan Dalar Amurka ta rage tsada da N3 a hannun ‘yan canji.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko 'Yan Najeriya sun gaji da Shugaba Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel