Alex Badeh, Olisa Metuh, da wasu 8 zasu gurfana gaban kotu a yau, 4 ga watan Yuli

Alex Badeh, Olisa Metuh, da wasu 8 zasu gurfana gaban kotu a yau, 4 ga watan Yuli

- Ana ci gaba da binciken rashawa a kan tsofafin masu rike da akalar gwamnati

- Tsofaffin gwamnoni 3 da kuma wani tsohon minister zasu gurfana a gaban kotu a yau, Talata, 4 ga watan Yuli

- Tsohon shugaban ma’aikatan tsaro, Alex Badeh ma zai gurfana

Wani rahoto daga TransparencIT Nigeria ya lissafo wasu shari’ar dake da alaka da cin hanci a kotu wanda za’ayi zaman su a yau, Talata, 4 ga watan Yuli.

A jarin sunayen akwai tsofaffin gwamnoni 3, Murtala Nyako na jihar Adamawa, Jolly Nyame na jihar Taraba da kuma Rasheed Ladoja na jihar Oyo.

Har ila yau wadanda zasu gurfana a gaban kotu a yau sun hada da tsohon shugaban ma’aikatan tsaro, Alex Badeh, tsohon sakataren labarai na jam’iyyar PDP, Cif Olisa Metuh da kuma tsohon ministan tarayya, Sanata Bala Mohammed.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Buhari ya rasu Inji wani Mawakin NajeriyaShugaban kasa Buhari ya rasu Inji wani Mawakin Najeriya

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) da hukumar yaki da cin hanci mai zaman kanta wato Independent Corrupt Practices Commission ne zasu jagoranci wadannan zama da aka lissafa a sama.

Kalli jerin sunaye a kasa:

Alex Badeh, Olisa Metuh, da wasu 8 zasu gurfana gaban kotu a yau, 4 ga watan Yuli

Jerin jamián da zasu gurfana gaban kotu a yau, 4 ga watan Yuli

Alex Badeh, Olisa Metuh, da wasu 8 zasu gurfana gaban kotu a yau, 4 ga watan Yuli

Alex Badeh, Olisa Metuh, da wasu 8 zasu gurfana gaban kotu a yau, 4 ga watan Yuli

A halin da ake ciki, mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya yi korafin cewa duk da kokarin da hukumar keyi, masu rashawa na shirya makirci kan yadda zasu ci gaba da satar kudin kasa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidyon gangamin hukumar yaki da cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel