Matasan Arewa da su ka ba Inyamurai wa’adi na shirin canza matsaya

Matasan Arewa da su ka ba Inyamurai wa’adi na shirin canza matsaya

– Jagoran Kungiyar ‘Arewa Youth Consultative Forum’ yace da sake

– Shugaban Kungiyar yace za su kara dubar lamarin korar Inyamurai

– Hakan na zuwa ne bayan da Shugabannin Inyamurai su kayi magana

Shugaban matasan nan na Arewa yace maganar korar Inyamurai daga Yankin da sake. Shettima Yerima ne ya ba Inyamuran wa’adi na su bar Arewa kwanakin baya wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce kasar.

Matasan Arewa da su ka ba Inyamurai wa’adi na shirin canza matsaya

Hoton wasu Matasan Arewa daga yanar gizo

Shugaban Kungiyar na ‘Arewa Youth Consultative Forum’ yace za su sake duba batun bayan Shugabannin Inyamurai sun fito sun soki matsayar masu fafutukar Biyafara. Hakan dai ya yiwu ne bayan wasu 'Yan Arewa sun nemi Inyamurai su bar masu Kasa.

KU KARANTA: Abin da ya sa Aisha Buhari ta tafi Landan

Matasan Arewa da su ka ba Inyamurai wa’adi na shirin canza matsaya

Hotunan 'Yan Arewa da Inyamurai daga NAIJ.com

Shettima yace sun ba Inyamuran kasar wa’adin ne ganin yadda Shugabannin Yankin Biyafara su kayi murus ba su taba Allah wadai da abin da wasu ke yi ba wanda yana iya jefa kasar gaba daya cikin matsala.

Shi ma Shugaban Kungiyar IPOB na Biyafara Nnmadi Kanu yayi amai ya lashe inda yace yanzu ya halatta Mutanen Biyafara su yi ibada a cocin Yarbawa dalili kuwa yanzu Yarbawan sun canza ba kamar da ba lokacin da ya nemi mutanen sa su kaurace masu.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dubi wani Bidiyo na Ojukwu da kuma Yakin Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel