Rundunar sojin Najeriya sun gano gurin kera makamai a Delta, an kama mutane 18

Rundunar sojin Najeriya sun gano gurin kera makamai a Delta, an kama mutane 18

- Rundunar Operation Delta Safe sun ce sun kai farmaki gurin kera bindigogin ne bayan wani rahoto

- Shugaban Operation Delta Safe, Rear Admiral Apochi Sulaiman, yace kamfanin suna kera makamai ga masu satar mutane, yan kungiyar asiri, yan fashi da makami na ruwa da kuma ýan bindiga

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun ta dake Niger Delta wato ‘Operation Delta Safe’ sun yi wani gagarumin kamu bayan sun kai farmaki makerar makamai.

A cewar rundunar sojin, makerar bindigogin na a Arhavwarien, yankin Ughelli dake jihar Delta.

An rahoto cewa an samo bindigogi da sauran makaman yaki bayan farmakin.

A cewar rundunar sunyi nasarar kai farmaki makerar ne bayan wani rahoto da suka samu na cewa kungiyar suna kera muggan makamai ga masu satar mutane, ‘yan kungiyoyin asiri, masu fashi da makami a ruwa, ‘yan bindiga da kuma masu fashi.

Rundunar sojin Najeriya sun gano gurin kera makamai a Delta, an kama mutane 18

Rundunar sojin Najeriya sun gano gurin kera makamai a Delta, an kama mutane 18

Rear Admira Apochi Suleiman, shugaban Operation Delta Safe, yayinda yake zantawa da yan jarida a Bayelsa, ya ce sun kama mutane 18.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Buhari ya rasu Inji wani Mawakin Najeriya

Ya ce an kama masu laifin ne bayan wasu laifuka daban-daban a yankin.

Ya ce daya daga cikin dabarun da suka yi amfani da jami’an sukayi amfani da shi shine odar makamai da dama daga wasu masu dillancin makamai da kira a matsayin Isiyaku Ochuko, Ese James da kuma Elvis Philips.

A halin da ake ciki, a baya NAIJ.com ta rahoto cewa an kasha mutane da dama sakamakon wani karo a karamar hukumar Yala, dake jihar Cross River.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com da shugabannin Najeriya suka yi magana game da Buiyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel