'Gwamnatin Buhari ta raba kan mutanen Najeriya' - Tsofafin ministocin PDP

'Gwamnatin Buhari ta raba kan mutanen Najeriya' - Tsofafin ministocin PDP

- Tsofafin ministocin jami’iyyar PDP sun dora alhakin rabe-raben da ke faruwa a kasar Najeriya akan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A wani taro da sukayi a gidan tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), tsofafin ministocin sun ce suna sa ran jami’iyyar PDP zata farfado daga barcin da ta ke shirga kafin zaben 2019.

'Gwamnatin Buhari ta raba kan mutanen Najeriya' - Tsofafin ministocin PDP

'Gwamnatin Buhari ta raba kan mutanen Najeriya' - Tsofafin ministocin PDP

Ku Karanta Kuma: Yanzu Yanzu, tsohon hadimi ga Janar Abacha ya rasu

A sakon da ya karanta bayan taron wanda aka shafe lokaci mai tsawo ana yi, Turaki yayi tir da halin da kasar nan ta sami kanta a yanzu na rashin tsaro, inda yace fashi da makami da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare. Ya hori gwamnatin tarayya da ta zage damtse wajen magance wannan matsalolin.

“Mahalarta taron sun dubi halin da kasar nan ta shiga da idon basira, babu tsaro a kasar musammamn idan akayi la’akari da yadda fashi da makami ke karuwa, garkuwa da mutane da kuma matsalar manoma da makiyaya da kan haifar da asaran rayuka, dukiyoyi da kuma gonaki.” Inji Turaki.

Ya kara da cewa rashin samun ingantaccen shugabanci ne daga gwamnatin Buhari ya haifar da rabe-raben kawuna mutane domin banbancin addini ko kabilanci.

“Mahalarta taron sun lura cewa babu wani lokaci a tarihin Najeriya da rabe-raben kai ya tsananta a dalinlin bambancin addini, yare da gari, kuma faruwan hakan abu ne mai ban takaici".

“Mahalarta taron sunyi kira da gwamnantin Buhari da ta dage wajen sauke nauyin mutane da ke kanta, kuma sunyi ma shugaba Buhari fatan samun lafiya domin ya dawo ya cigaba da ayyukan sa a matsayin shugaban kasar Najeriya.” Inji Turaki

A abin da yayi kama da rashin da’a ga shugabancin Ali Modu Sheriff a jami’iyyar, mahalarta taron sun nuna gamsuwa da goyon bayan su shugabancin wucin gadi dake karkashin jagorancin Senata Ahmed Makarfi.

Sai ku biyo mu a shafukan sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel