Assha! Yadda dafadukar shinkafa ta kashe mutane 5 a gida daya a Najeriya

Assha! Yadda dafadukar shinkafa ta kashe mutane 5 a gida daya a Najeriya

- Wasu iyalai a jihar Imo su 5 sun halaka bayan cin shinkafa dafaduka

- Wannan al'amari dai ance ya faru ne a wani kauye da a cikin karamar hukumar Isiala Mbano

- Uwa da uba da kuma yayayen su 3 ne dai suka mutu bayan cin abin cin

Wannan al'amari dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu ya faru ne a cikin jihar Imo dake kudancin Najeriya inda iyalai mai mutane 5 suka mutu ringis bayan sun ci shinkafa dafa duka.

Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa matar mai gidan kuma uwar yayan mai suna Nwosu Obianuju itace ta dafa shinkafar da kanta wadda tayi ajalin ita kanta da mijinta da kuma yayan nasu su 3.

Assha! Yadda dafadukar shinkafa ta kashe mutane 5 a gida daya a Najeriya

Assha! Yadda dafadukar shinkafa ta kashe mutane 5 a gida daya a Najeriya

NAIJ.com ta samu labarin cewa yayin da yake magana da manema labarai, dan mamatan na fari Chukwuemeka Nwosu, ya bayyana cewa ba ya gida a lokacin da abun ya faru, amma ya yi kira ga jami’an tsaro da su zurfafa bincike akan lamarin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel