Garabasa! Hukumar Kwastam ta kasa ta fara gwanjon motocin da ta kwace a yanar gizo

Garabasa! Hukumar Kwastam ta kasa ta fara gwanjon motocin da ta kwace a yanar gizo

- Hukumar Kwastam ta kasa ta fara gwanjon motocin da ta kwace a yanar gizo

- Shugaban hukumar Kanal Hamid Ali mai ritaya shine ya bayyana hakan a lokacin da ya kaddamar da shafin yanar gizon

- Kanal Hamid Ali ya bukaci duk mai so ya je ya kwashi rabon sa

Shugaban hukumar Kwastam ta kasa Kanal Hamid Ali mai ritaya ya kaddamar da shafin yanar gizo na hukumar wanda aka fara gwanjon motocin da hukumar ta kwace.

An dai fara wannan gwanjon ta shafin ne a jiya litinin da karfe 12 na rana.

Da yake bayani bayan ya bude shafin, Kanal Hamid Ali ya bayyana hakan a matsayin wata babbar nasar da hukumar ta samu wadda zatayi maganin cin hanci da rashawa da kuma korafe-korafe daga jama'a da dama.

Garabasa! Hukumar Kwastam ta kasa ta fara gwanjon motocin da ta kwace a yanar gizo

Garabasa! Hukumar Kwastam ta kasa ta fara gwanjon motocin da ta kwace a yanar gizo

NAIJ.com ta samu labarin cewa Hamid Ali yace a da dai sai wadan da suka san wani a hukumar kawa suke samun wannan garabasar amma yanzu kowa zai iya samu idan har yayi siyan mutunci kuma ba tare da wata rashawa ko cin hanci ta shigo ciki ba.

Tun dai da Hamid Ali din ya hau mukamin nasa ba'a taba yin gwanjon ba sai a wannan karon.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel