Ba zamu bi arewa ko kudu ba idan Najeriya ta wargaje - Inji yan asalin Abuja

Ba zamu bi arewa ko kudu ba idan Najeriya ta wargaje - Inji yan asalin Abuja

- Wata kungiya ta yan asalin garin Abuja tace suma zasu kafar kasar su idan Najeriya ta wargaje

- Kungiyar tace ba za ta bi kowane bangare ba amma zasu kafa kasar su suma

- Kungiyar tace zata kira taron koli na yan asalin garin na Abuja nan ba da dadewa ba

Wasu mazauna garin Abuja babban birnin Najeriya karkashin wata kungiya mai suna Original Inhabitants Development Association (OIDA) a turance sunce suma zasu kafa kasar su idan har Najeriya ta wargaje.

Yan kungiyar sunce a maimakon su bi arewacin kasar kokuma kudu suma zasu zabi su kafa kasar su ne ta hanyar bin yadda tsari yake.

Ba zamu bi arewa ko kudu ba idan Najeriya ta wargaje - Inji yan asalin Abuja

Ba zamu bi arewa ko kudu ba idan Najeriya ta wargaje - Inji yan asalin Abuja

NAIJ.com ta samu labarin cewa kafin hakan dai, yan kungiyar sun jadda bukatar ganin cewa kasar Najeriya ta zauna lafiya ta kuma goyi bayan zama a kasa daya.

Amma kuma sai suka ce idan har yiwuwar rushewar Najeriya ta taso to tabbas suma zasu yankin rabon su su kuma bukaci majalisar dinkin duniya ta mulke har ya zuwa wani dan lokaci.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel