Kungiyar ma'aikatan makarantun fasahohin kasar nan sun kira taron gaggawa game da matsalar albashin su

Kungiyar ma'aikatan makarantun fasahohin kasar nan sun kira taron gaggawa game da matsalar albashin su

- Kungiyar ma'aikatan makarantun fasahohin kasar nan watau ASUP sun kira taron gaggawa na ya'yan kungiyar

- Kungiyar ta kira taron ne saboda matsalar albashin da ya'yanta ke ciki

- Shugaban kungiyar ta kasa Kwamared Usman Dutse ya bayyana wa manema labarai hakan a Abuja

Shugabancin gudanarwar kungiyar ma'aikatan makarantun fasahohin kasar nan watau Academic Staff Union of Polytechnic (ASUP) a turance sun kira taron gaggawa na ya'yanta saboda matsalar albashin da suke fama da ita.

Shugaban kungiyar Kwamared Usman Dutse ne ya shaidawa manema labarai hakan a garin Abuja inda yace ya zuwa yanzu gwamnati ta zama makaryaciya kuma su basu kara yadda da iya.

Kungiyar ma'aikatan makarantun fasahohin kasar nan sun kira taron gaggawa game da matsalar albashin su

Kungiyar ma'aikatan makarantun fasahohin kasar nan sun kira taron gaggawa game da matsalar albashin su

NAIJ.com ta samu labarin cewa Shugaban na kungiyar har ilayau ya bayyana cewa jihohin kasar nan da kuma gwamnatin tarayya duka sun dauke su kananan mutane don kuwa duk da makudan kudaden da suka samu har yanzu sunki biyan su hakkokan su yadda ya kamata.

A cewar sa hakkokan sun hada da kudaden hutu, kudaden karin girma da kuma kudaden nan da ake ba duka wani sabon ma'aikaci.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel