Rashin lafiyar buhari ya tsananta, dole ya yi murabus – Fayose ya maida martani ga komawar Aisha Landan

Rashin lafiyar buhari ya tsananta, dole ya yi murabus – Fayose ya maida martani ga komawar Aisha Landan

- Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya ce komawar Aisha Buhari Landan ya wanke shi daga tuhuma

- Fayose ya nace kan cewa lallai ya kamata shugaban kasar ya yi murabus kamar yadda ya fada a lokacin da Yar’Adua ke fuskantar irin wannan matsalar

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya nace kan cewa lallai shugaban kasa Muhammadu buhari na nan bai san inda kansa yake ba, ya kara da cewa wannan ne yasa matarsa, Aisha ta koma Landan.

Buhari ya kasance a birnin Landan don jinya sannan kuma Aisha ta ziyarce shi sau biyu cikin kasa da makonni uku.

Fayose ya ce gaggawan da Aisha tayi na kuma barin Najeriya ya tabbatar da cewa yana da gaskiya da ya yi ikirarin cewa shugaban kasar na nan bai san inda yake ba.

Rashin lafiyar buhari ya tsananta, dole ya yi murabus – Fayose ya maida martani ga komawar Aisha Landan

Rashin lafiyar buhari ya tsananta, dole ya yi murabus – Fayose ya maida martani ga komawar Aisha Landan

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Buhari ya rasu Inji wani Mawakin Najeriya

“Kwananki shidda kenan da nayi jawabi ga manema labarai sannan a yau, ina nan akan bakana na cewa shugaban kasar na nan bai san inda kansa yake ba” cewar Fayose a wata sanarwa daga mataimakin sa, Lere Olayinka.

A wata sanarwa da NAIJ.com ta samu, Fayose, wanda ya yi jawabi ga wasu yan jarida a Lagas a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli, ya ce: “tabarbarewar rashin lafiyar shugaban kasa ne ya sa Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari gaggawan tafiya Landan sannan kuma ana sa ran cewa zata dawo ta fada ma ‘yan Najeriya gaskiya a wannan karo.

“Babu wanda ke son mutuwar shugaba Buhari. Maimakon haka, muna son ceto Najeriya daga hannun ‘yan tsirarun mutane wanda a yanzu suke rike da kasar."

Gwamnan ya bukaci cewa lallai ya zama dole shugaban kasar ya yi murabus.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Gwamana Rochas Okorocha na jihar Imo, da yake maida martini ga ikirarin Fayose na cewa shugaban kasar na nan bai san inda yake ba, ya bukaci yan Najeriya da suyi watsi da takwaran nasa.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan Fayose ya tsaya takaran shugabancin kasa a yau, zaka zabe shi? Kalli wannan bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel