Tsugune bata kare ba: Koriya ta Arewa ta sake kaddamar da makami mai linzami

Tsugune bata kare ba: Koriya ta Arewa ta sake kaddamar da makami mai linzami

- Kasar Koriya ta Arewa ta harba wani sabon makami mai linzami

- Makamin dai ance yayi tafiyar mintuna 40 kafin ya fadi

- Tafiyar da makamin yayi dai ta nuna cewa zai iya shiga kasar Amurka

Kasar Koriya ta Arewa dake da makwaftaka da ta Koriya ta Kudu a yankin Asiya ta sake yin wani gwajin ta da ta saba na makami mai linzami.

A wannan karon kuma makamin da suka harba an ruwaito cewa yayi tafiyar da ta kai mintuna 40 kafin ya fadi. Hakan dai ya nuna karara cewa ta kara inganta makamin nata ne inda wannan yafi ko wane inganci.

Tsugune bata kare ba: Koriya ta Arewa ta sake kaddamar da makami mai linzami

Tsugune bata kare ba: Koriya ta Arewa ta sake kaddamar da makami mai linzami

NAIJ.com ta samu labarin cewa kasar Amurka tuni tayi tir da wannan matakin na Koriya ta Arewa inda ta bayyana shi a matsayin takalar fada kawai.

A baya dai mai karatu zai iya tuna ayi ta kai ruwa rana game da shirin na Koriya ta Arewa dangane da mallakar makamin na Nukiliya mai linzami.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel