Dino Melaye: Cikin Dino ta debi ruwa, hukumar zabe za ta fara yi masa kiranye

Dino Melaye: Cikin Dino ta debi ruwa, hukumar zabe za ta fara yi masa kiranye

- Hukumar zabe ta nanar cewa za ta fara yiwa sanata Dino Melaye kiranye kamar yadda masu jefa kuri’a a mazabarsa suka bukata

- INEC ta sa ranar 3 ga watan Yuli a matsayin ranar da zata aiwatar da kiranyen sanatan

- Sanata Melaye ya kalubalanci yunkurin yi masa kiranye a kotu

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli ta saki lokacin da za a fara yiwa sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Dino Melaye kiranye daga majalisar dattijai.

Wannan na zuwa ne dai dai da lokacin da lauyan dan majalisar ke kokarin dakatar da hukumar.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, a makon da ta gabata ne hukumar zabe ta sanar da samun wata takarda daga mazabar sanata Melaye inda mutanen ke neman masa kiranye. Fiye da 52 cikin 100 na masu jefa kuri'a a mazabar suka sanya hannu a kan takarda rajistar mazabar.

Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Dino Melaye

Dino Melaye: Cikin Dino ta debi ruwa, hukumar zabe za ta fara yi masa kiranye

Hukumar ta kuma rubuta wa sanatan inda ta sanar da shi samu takardar masa kiranye kuma ta ce zata fara aiwatar a ranar 3 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Bamu san gaskiyar halin da lafiyar shugaba Buhari ke ciki ba - APC

Sanata Melaye ta hanyar lauyarsa Mike Ozekhome ya kai kara a babbar kotun tarayya da ke Abuja inda yake kalubalantar yunkurin yi masa kiranye.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel