Shugaban kasa Buhari ya rasu Inji wani Mawakin Najeriya

Shugaban kasa Buhari ya rasu Inji wani Mawakin Najeriya

– Wani Mawakin Najeriya da ke kasar waje yace Shugaba Buhari ya cika

– Haka kuma Mawakin yace yana da burin zama Shugaban kasar Biyafara

– Kwanan nan ne dai Mawaki Speed Darlington ya fara fice a Duniya

Wani Mawakin kasar nan yake cewa Shugaban kasa Buhari ya rasu. Har da godewa Ubangiji Mawakin yayi bayan ya bayyana wannan. Sai dai babu wata hujja ko kusa da ke tabbatar da hakan.

Shugaban kasa Buhari ya rasu Inji wani Mawakin Najeriya

Hoton Mawakin Najeriya daga shafin Instagram

Speed Darlington wani Mawakin Najeriya ne da ke zaune a kasar Amurka yayi ikirarin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu. Mawakin har da godewa Ubangiji yayi bayan ya rubuta wannan a shafin sa na Instagram.

KU KARANTA: Buhari ya aikowa Gwamnan Kano wasikar ta'aziyya

Shugaban kasa Buhari ya rasu Inji wani Mawakin Najeriya

Hoton Buhari bai da lafiya daga fadar Shugaban kasa

Mawakin mai tasowa ya kuma bayyana cewa yana da niyyar zama Shugaban kasar Biyafara na farko da zarar Kasar ta samu. Wasu dai daga cikin ‘Yan kasar na ta fafutukar ganin Kudancin kasar sun balle daga Najeriya.

Kwanan nan Mista Ayo Fayose Gwanan Ekiti yace Shugaba Buhari ko numfashi ba ya iya yi wanda hakan ya sa Jama’a da dama su ka dura kan sa, wanda har ‘Yan Jam’iyyar adawa ba su raga masa ba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Najeriya sun yi kwanaki sama da 50 ba a san inda Buhari yake ba [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel