Yadda Obasanjo ya kashe PDP Inji Tsohon Kakakin Majalisa

Yadda Obasanjo ya kashe PDP Inji Tsohon Kakakin Majalisa

– A cewar Dimeji Bankole tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya kashe PDP

– Tsohon Kakakin Majalisar kasar ya bayyana haka a Garin Abeokuta

– Dimeji Bankole dai ya tsere daga PDP zuwa wata sabuwar Jam’iyya ADP

Jam’iyyar PDP mai adawa yanzu dai tana cikin wani rikici. Kwanan nan Doyin Okupe ya bayyana cewa ya bar PDP. Doyin Okupe yayi aiki da tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Yadda Obasanjo ya kashe PDP Inji Tsohon Kakakin Majalisa

Hoton tsohon Shugaban kasa Obasanjo daga yanar gizo

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Dimeji Bankole ya bayyana cewa tsohon Shugaban kasar nan Cif Olusegun Obasanjo ya fara jawo abin da ya kashe Jam’iyyar PDP domin gudun wasu su yi karfi a Jam’iyyar lokacin. Yanzu dai Bankole sun wata sabuwar Jam’iyya mai suna ADP

KU KARANTA: APC ba ta san yadda Shugaba Buhari yake ciki ba

Yadda Obasanjo ya kashe PDP Inji Tsohon Kakakin Majalisa

Hoton tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Bankole daga NAIJ.com

Bankole ya bayyana haka ne a Garin tsohon Shugaban kasar na Abeokuta da ke Jihar Ogun. Yake cewa Obasanjo yayi kokarin hana Gwamnoni zama Shugabannin Jam’iyyar a Jihohin su wancan lokaci wanda hakan ya haifa matsala.

Kwanan nan Dr. Doyin Okupe ya bayyana cewa yaga rikicin PDP bai da karshe don haka ya sulale ya bar ta. Doyin Okupe yayi aiki da tsohon shugaban kasa Obasanjo da kuma Goodluck Jonathan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gobara ya kama wani gida da ke saman dutse

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel