Jagoran ‘Yan tawaye Nnamdi Kanu ya caccaki Shugaba Buhari

Jagoran ‘Yan tawaye Nnamdi Kanu ya caccaki Shugaba Buhari

– Jagoran Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu ya soki Shugaban kasa

– Nnamdi Kanu ya bayyana abin da ya sa ya saba dokar Kotu

– An gindaya masa wasu sharuda lokacin da aka bada belin sa

Nnamdi Kanu ya bayyana dalilin da ya sa ya saba sharudan da aka gindaya masa. A cewar sa ai Shugaban kasa Buhari ma yana da laifi wajen saba dokar Kotu. Nnmadi Kanu ya zargi Gwamnatin Buhari da kin sakin wadanda ake zargi daga kaso.

Jagoran ‘Yan tawaye Nnamdi Kanu ya caccaki Shugaba Buhari

Hoton Jagoran IPOB Nnamdi Kanu daga NAIJ.com

Bayan Jagoran na Kungiyar IPOB ta Biyafara ya zargi Shugaban kasa Buhari da saba umarnin Kotu wajen hukuncin El-Zakzaky da Dasuki kamar yadda shi ma karan-kan sa yayi ya kuma ce babu wanda zai yi zabe a Jihar Anambra.

KU KARANTA: Sojin kasa na bayan Buhari Inji Janar Buratai

Jagoran ‘Yan tawaye Nnamdi Kanu ya caccaki Shugaba Buhari

Hoton Nnamdi Kanu da Shugaba Buhari daga NAIJ.com

Nnmadi Kanu ya kuma yi amai ya lashe inda yace yanzu ya halatta Mutanen Biyafara su yi ibada a cocin Yarbawa dalili kuwa yanzu Yarbawan sun canza ba kamar da ba lokacin da ya nemi mutanen sa su kaurace masu.

Wasu Inyamurai da ke kasar waje sun yi kaca-kaca da Jagoran Biyafara Nnamdi Kanu su kace bai isa yayi magana da yawun su ba. Inyamuran su kace babu wanda ya sa ko ya isa yayi magana da bakin Inyamuran Duniya.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani bidiyo game da Ojukwu lokacin Yakin Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel