Ta’aziyar Dan Masani: Buhari ya aikawa Gwamnan Kano wata wasika mai ban tausayi

Ta’aziyar Dan Masani: Buhari ya aikawa Gwamnan Kano wata wasika mai ban tausayi

- Shugaba Buhari ya aiko takarda inda yake takaicin rashin Maitama Yusuf

- An yi babban rashi a Najeriya gaba daya Inji Shugaban kasa Buhari

- Tsohon Ministan Kasar ya rasu ne Jiya a Asibiti da ke kasar Masar

Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wasika ga Gwamnan Kano Dr. Ganduje. Shugaban Kasar yana ta’aziyya ne ga Jama’ar Kano duka game da rashin Dan Masani. Dan Masanin Kano mutum ne mai baiwar magana har bayan ya makance Inji Buhari.

Ta’aziyar Dan Masani: Buhari ya aikawa Gwamnan Kano wata wasika mai ban tausayi

Hoton Dan Masanin Kano tare da Buhari daga Jaridar NigerianMonitor

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikowa Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje wasikar ta’aziyar tsohon Ministan Najeriya kuma Dattijon Arewa Yusuf Maitama Sule. Shugaba Buhari yace an yi babban rashi a Najeriya.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa ba za a taba mantawa da Dan Masani ba

Ta’aziyar Dan Masani: Buhari ya aikawa Gwamnan Kano wata wasika mai ban tausayi

Hoton Dan Masani da Buhari da Gwamnan Kano daga NAIJ.com

Shugaba Buhari yace Marigayin ya taimakawa Shugabannin Najeriya na farko a lokacin yana Minista. Har ya bar Duniya ba a taba samun sa da wani rashin gaskiya ba. Shugaba Buhari yace har ya bar Duniya yana koyon darasi wajen Dan Masanin Kano idan su ka zauna.

A jiya ne shi ma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya taya sauran Jama’a ta’aziyar Marigayi Ambasada Yusuf Maitama Sule da ya cika. Gwamnan yace an yi babban rashi a Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kwanaki 50 baya 'Yan Najeriya sun fara tambayar inda Buhari ya shige

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel