Ban da hannu a karan rundunar ‘yan sandan Najeria – Inji Evans

Ban da hannu a karan rundunar ‘yan sandan Najeria – Inji Evans

- Madugun da ake zargi da garkuwa da mutanen nan ya karyata cewa shine ya bada izinin kai rundunar ‘yan sanda Najeriya kara

- Lauya Olukoya Ogungbeje ya bukaci a biyar Evans miliyan 300 a matsayin kudin diyya

- Evan ya ce wannan wani yunkuri na wasu mutane ne domin su kara jefa shi cikin wani tarko

Madugun da ake zargi da garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka sani da Evans ya nisanci kansa daga karan ‘yan sanda da wani lauya mai suna Olukoya Ogungbeje ya yi a madadinsa a babbar kotun tarayya da ke birnin Legas.

A cikin karan biyu da Ogungbeje ya kai gaban kotu, ya bukaci a biyar Evans miliyan 300 a matsayin diyya kan yadda 'yan sanda suka tsare shi ba bisa doka ba.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, a lokacin da yake magana da gidan talabijin na Channel inda yake tsare, Evans ya muzanta zargin cewa shine ya sa a kai kara a kotu, ya ce wannan wani yunkuri na wasu mutane ne domin su kara jefa shi cikin wani tarko.

Ban da hannu a karan rundunar ‘yan sandan Najeria – Inji Evans

Madugun da ake zargi da garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka sani da Evans

Ya ce: "Ban da hannu a cikin karan 'yan sanda da aka kai kotu kuma ban yi magana da wani lauya ko mahaifina ba”.

KU KARANTA: Dansanda ya kiɗime, ya harbi kansa, yayi ƙoƙarin bindige kwamishinan Yansanda

Evans ya ci gaba da cewa idan ‘yan sanda suka sake shi, shaka babu ba zai tafi ba saboda mutanen da ya sace kuma ya karba miliyoyin kudin fansa a hannun su zasu kashe shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel