An cafke wasu ‘yan kuna bakin wake a tsakanin ‘yan gudun hijira

An cafke wasu ‘yan kuna bakin wake a tsakanin ‘yan gudun hijira

- Wasu mayakan 'yan kuna bakin wake shiga hannu sojojin a sansannin 'yan gudun hijira

- Akala 'yan kungiyar Boko Haram 9 da kuma masu taimaka musu 100 suka yi badda kama a tsakanin daruruwan 'yan gudun hijira

- Jami’an tsaro sun gano wadannan mayakan ne a lokacin da suke tantance ‘yan gudun hijirar a garin banki

Ma’aikatar bada agajin gaggawa ta jihar Borno ta bayyana a ranar Asabar, 1 ga watan Yuli cewa ta gano wasu mayakan kungiyar Boko Haram da suka yi badda kama a tsakanin daruruwan 'yan gudun hijira wadanda ke komawa arewa maso gabashin Najeriya daga kasar Kamaru.

NAIJ.com ta tattaro cewa shugaban hukumar ta SEMA shiyar Borno, Ahmad Satomi, ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa akala 'yan kungiyar Boko Haram 9, da wasu da ake zato cewa suna taimaka musu su 100 aka damke a tsakanin ‘yan gudun hijirar 920 da suka koma gida daga garin Marwa da ke kasar Kamaru.

KU KARANTA: Muna bayan Buhari dari bisa dari – Inji babban hafsan sojan Najeriya

Shugaban hukumar ya bayyana cewa an samu wannan nasarar ce a lokacin da jami’an tsaron Najera suke tantance ‘yan gudun hijirar a garin banki da ke kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru.

An cafke wasu ‘yan kuna bakin wake a tsakanin ‘yan gudun hijira

Daruruwan 'yan gudun hijira wadanda ke komawa arewa maso gabashin Najeriya daga kasar Kamaru

Hukumar SEMA shiyar jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta bayyana cewa, mai yiwuwa mutane 100 da aka tsare tare da ‘yan Boko Haram din, 'yan ta'addan sun tilasta musu yi wa kungiyar aiki ne, a lokacin da kauyukansu suka kasance a karkashin mamayar mayakan.

Satomi ya ce har zuwa yanzu an tantance mutane 800 daga cikin wadanda suka koma gida.

A makon da ta gabata ne Kasar Kamaru ta dawo da wasu ‘yan Najeriya da suka tsere wa rikicin Boko Haram su 887 zuwa garin Banki, wanda ke iyakar kasashen Kamaru da Najeriya.

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa a kan yadda Kamaru ke tilasta 'yan gudun hijira daga kasar zuwa Najeriya.

A ranar Litinin ne babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce fiye da 700 'yan ta'adda Boko Haram suka mika wuya ga jami'an tsaro a dajin Sambisa kuma akwai wasu masu shirin mika wuya nan gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel