Aikin Hajji: An bukaci mahajjata da su yi hankuri da farashin kudaden kujeran Hajjin bana

Aikin Hajji: An bukaci mahajjata da su yi hankuri da farashin kudaden kujeran Hajjin bana

- Hukumar kula da ayyukan Hajji na Najeriya ta yi taron bikin cika shekaru 10

- Hukumar ta bukaci mahajjatan Najeriya da su yi hankuri da farashin kudaden kujeran Hajjin bana

- Bello Tambuwa, babban sakataren hukumar Alhazan ya ce tashin farashin dalar Amurka data ci karfin naira yasa farashin kudaden kujeran haka

An yi bikin cika shekaru 10 da kafa hukumar kula da ayyukan Hajji na Najeriya wato NAHCON.

Kamar yadda muryar Amurka ta ruwaito, an dai shafe kwanaki 2 ana gudanar da wannan taro da kuma bita akan yadda za a inganta aikin Hajji wanda ako wane shekara ake kokarin bunkasa shi.

Babban jami’in watsa labarai na hukumar ayyukan Hajji na Najeriya, Malam Uba Mana ya ce: ‘’ Yanzu haka hukuman Alhazan ta kai shekaru 10 kuma muna muna a kan wasu ci gaba da hukumar ta samu tun da aka kagfa ta, saku ganin cewa abin yabo ne domin hukumar ta aiwatar da abubuwa da dama alal misali a yanzu ba zaka ji wani ya ce an bar wani daga cikin Alhazan Najeriya a tashar jirgi ba, ba zaka ji cewa an samu jinkiri a lokacin da ya kamata a kai Alhazan ba, ba zaka ji gwamnatin tarayyar Najeriya na rokon gwamnatin kasar Saudiya ta bamu lokaci ko mu dauki Alhazan mu zuwa gida Najeriya ko kuwa mu kaisu Saudiyya ba, a yau ba zaka ji ana kukan cewa jirgi ya kaza ya bar mutane kaza ba, ba zaka ji jiragen kanfanonin yawo sun cuci wani ba tare da hukumar Alhazai ta shigo ta mangance wannan abu ba, abubuwa da dama gaskiya sai hamdala’’.

Aikin Hajji: An bukaci mahajjata da su yi hankuri da farashin kudaden kujeran Hajjin bana

Wasu daga cikin Mahajjatan Najeriya

Ko da yake jawabin bayan taron ya nuna cewa korafe-korafen mutane kan ya kamata a rage kudin Hajjin bana bai samu karbuwa ba saboda hauhawar musayar kudi ta naira da kuma dalar Amurka da ake amfani dasu.

KU KARANTA: Rasuwan dattijon arziki, Alh Yusuf Maitama Sule: Munyi rashin babban ginshiki a tarihin kasarmu – Sanata Shehu Sani

NAIJ.com ta tattaro cewa, sakataren hukumar Bello Tambuwa ya ce tashin farashin dala data ci karfin naira ya sanya dole ayi hankuri da wannan farashi na kudaden kujeri manya da kuma kanana na Mahajjata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel