Muna bayan Buhari dari bisa dari – Inji babban hafsan sojan Najeriya

Muna bayan Buhari dari bisa dari – Inji babban hafsan sojan Najeriya

- Rundunar sojojin Nijeriya ta ce tana bayan gwamnatin shugaba Buhari dari bisa dari

- Rundunar ta ce zata iya kare 'yancin yankunan kasar a duk lokacin da ta fuskanci barazana

- Buratai ya ce sojojin kasar zasu yi biyayya ga shugaban kasar Muhammadu Buhari

Rundunar sojojin Nijeriya a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli ta sake jaddada biyayyar ta ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari cewa tana bayan gwamnatin dari bisa dari.

Rundunar ta ce zata iya kare 'yancin yankunan kasar a duk lokacin da ta fuskanci barazana.

Babban hafsan sojojin Najeriya, Lt Janar Tukur Buratai ya bayyana hakan ne a wani taron addu’an tunawa da ranar sojojin Najeriya wanda aka gudanar a cocin All Saints 'Military Church, wanda ke barikin sojan Mogadishu Cantonment a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Buratai ya dage da cewa sojojin kasar a karkashin jagorancinsa, zasu yi biyayya ga shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Muna bayan Buhari dari bisa dari – Inji babban hafsan sojan Najeriya

Babban hafsan sojojin Najeriya, Lt Janar Tukur Buratai

NAIJ.com ta ruewaito cewa, Buratai wanda Manjo Janar Chris Jemitola, shugaban aiwatar da manufofi da kuma tsare-tsaren na hedkwatar sojojin Najeriya ya wakilta, ya tabbatar wa sojojin cewa ofishinsa ta dauka da muhimmanci al'amurran da suka shafi jindadin da kuma horos da su.

KU KARANTA: Sakona ga arnan duniya, yanzu zaku fara ganinmu a kan ku – Cewar karamin yaro dan Boko Haram (Bidiyo)

A wata rahoto, babban hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya bayyana cewa fiye da 700 'yan ta'adda Boko Haram suka mika wuya ga sojojin na Operation Lafiya Dole da ke Borno.

Buratai ya ci gaba da cewa akwai sauran mayakin da ke shirin mika wuya nan gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel