Boko Haram: Fiye da 700 'yan Boko Haram sun mika wuya – Inji Babban hafsan sojojin Najeriya

Boko Haram: Fiye da 700 'yan Boko Haram sun mika wuya – Inji Babban hafsan sojojin Najeriya

- Fiye da 700 ‘yan kuna bakin wake sun mika wuya a dajin Sambisa da ke jihar Borno

- Babban hafsan Sojojin Najeriya ya ce akwai ‘yan kungiyar Boko Haram da dama masu shirin mika wuya nan gaba

- Buratai ya ce yana taya jarumai rundunar sojojin Najeriya murnar wannan nasarar da suka samu a kan kungiyar Boko Haram

Babban hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai a yau Litinin, 3 ga watan Yuli, ya bayyana cewa fiye da 700 'yan ta'adda Boko Haram suka mika wuya ga sojojin na Operation Lafiya Dole da ke Borno.

Mika wuyar da wadannan ‘yan kuna bakin waken suka yi kamar yadda Buratai ya bayyana ya biyo bayan ci gaba da kai wa matsugunin ‘yan ta’addan hari a sassan na dajin Sambisa da sojojin Najeriya ke yi da hadin gwiwar sojojin sama.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, Buratai ya ce ko yanzu haka akwai ‘yan kungiyar Boko Haram da dama wadanda ke shirin mika wuya ga rundunar sojojin Najeriya nan gaba, babban hafsan sojan ya ce wannan ci gaba ne kuma zai iya kawo kwanciyar hankali ga al’ummman yankin da kuma Najeriya baki daya.

Boko Haram: Fiye da 700 'yan Boko Haram sun mika wuya – Inji Babban hafsan sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya

KU KARANTA: Kisan kare-dangi aka yi wa ‘Yan Fulani a Mambilla Inji Sojin Najeriya

" Wannan ya nuna cewa mun ci galaba a kan yaki da ‘yan kunar bakin wake Boko Haram. Ina taya jarumai rundunar sojojin Najeriya har da na sama da na ruwa murnar wannan nasarar da kuma duk 'yan Najeriya”. A cewar Buratai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel