Masu kananan jiragen sama na yawon shakatawa zasu sha bincike

Masu kananan jiragen sama na yawon shakatawa zasu sha bincike

- Ana zargin da yawa daga masu hawa jiragen yawo kanana na alfarma da kudaden haram aka saye su.

- Hukumar haraji ta kasa tace zata bi diddigin ko masu jiragen suna biyan haraji

- Yawa-yawan jiragen dai an ma tsere dasu daga Najeriya an yi musu sabuwar rajista a kasashen waje.

Najeriya, kasa ce mai umbin arziki da aka sace wa kudade a lokuta da dama aka kai kasashe waje, ake kuma bushasha dasu a kan idon talakka. An gano yawa-yawan jiragen yawo na hamshakan masu kudi sun tsere dasu daga Najerya tun bayan hawan gwamnatin APC, inda aka gano kusan 40 an kaisu kasar Afirka ta kudu an musu sabuwar rajista.

Sai dai, hakan baya nufin sun sha, domin a yanzu, hukumar haraji ta kasa, FIRS, ta sha alwashin bin kadin inda aka karkata akalar jiragen da kuma bin kadin makuan kudaden haraji da suka tsallake basu biya lalitar gwamnati ba.

KU KARANTA KUMA: Bamu san gaskiyar halin da lafiyar shugaba Buhari ke ciki ba - APC

Masu kananan jiragen sama na yawon shakatawa zasu sha bincike

Masu kananan jiragen sama na yawon shakatawa zasu sha bincike

A cewar kakakin hukuma, batun ba ma na a ji ko kudaden halas ne suka sayi jiragen ba, ko kuma aá, yace yanzu ta haraji suke, aga yadda zasu biya basukan baya, kuma su biya na gaba, koda kuwa sun shallake sun gudu wata kasar.

Rahoton baya-bayan nan dai ya bada yawan jiragen da suka yi rajista a Afirka ta kudu har 39, wasu kuma sun koma kasashen turai.

Abin takaicin dai shine, ko yaushe kuma zaá duba a ga ko akwai jinin talakka a kudin jiragen in kuma hakan ne, yaushe zasu dawo su zame wa talaka wani gata ta wata hanyar.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Twitter: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel