Buratai yace suna dab da kamo Abubakar Shekau na Boko Haram

Buratai yace suna dab da kamo Abubakar Shekau na Boko Haram

- An dade ana 'kashe' shugaban Boko Haram amma gawa taki rami

- An dade ana cewa an gama da kungiyar myakan Boko Haram amma har yanzu tsugunne bata kare ba

- Shugaban Sojin Najeriya yace suna kan bakansu na kama shugaban Boko Haram

A kokarin gwamnati da hukumar sojin Najeriya na kakkabe burbushin taáddanci a Najeriya, shugaban sojin Najeriya yace suna kan bakansu na kame shugaban wani bangare na Boko Haram, wato Sheikh Abubakar Shekau.

A zantawarsa da manema labarai, Janar Tuur Buratiai yace suna kan kokarin da suke na kame Abubakar Shekau, idan sun kutsa dajin Sambisa, inda suke zargin shugaban a nan yake boye. A cewarsa, zasu ada kai da ýansandan yankin don sake kafa sabbin sansanoni a cikin dajin domin kame wuraren da ýan taáddan ke fakewa su kai hari.

KU KARANTA KUMA: Gowon ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya

Buratai yace suna dab da kamo Abubakar Shekau na Boko Haram

Buratai yace suna dab da kamo Abubakar Shekau na Boko Haram

A baya dai, sojin Najeriya, sunsha jin kunyar cewa sun hallaka shugaban mayakan, amma sai ya fitar da sabon faifan bidiyo yana yi musu izgili.

A yanzu dai baá san inda shi shugaban yake ba, duk da sanarwar da ya fitar ta baya-bayan nan cewa sun kame mata ýansanda kuma ma sun sayar dasu.

A lokuta da dama dai ana kame manyan kwamandojin Boko Haram, amma ana sakin wasu yayin da ake sulhu dasu domin wasu da suka kame suka bautar.

A shekarar 2015 ma shugaban kasar Chadi Idris Debi yayi barazanar ko Abubakar Shekau y fito ya mika kansa ko kuma su far ma maboyarsa, domin wai sun gano inda yake, baá kara jin wannan batu ba, inda ya tashi a barazana ga kwadi.

A yanzu dai Buratai yace baza su tona irin sabon salonsu ba, har sai sun cimma burinsu, domin kada magabta su ankara su sabe. Ya kuma bada yawan adadin jamián tsaron da ke yankin, ko hakan zai yi tasiri, sai ku biyo mu;

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Twitter: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel