Namadi Sambo ya koka kan yawan tsangwamar jami'an EFCC kan dukiyarsa

Namadi Sambo ya koka kan yawan tsangwamar jami'an EFCC kan dukiyarsa

- Tsohon mataimakin shugaba Jonathan na shan bincike

- An sha kai samame gidan Namadi Sambo amma babu abin da aka samu

- A 2015, an kwashe dalolin na kudi daga ofishin Namadi Sambo a Abuja

Tun bayan samamen hukumar bincike da taánnati da kudin kasa kan gidan Namadi Sambo a jihar Kaduna, an jiyo martani daga hukumomi na yansanda, a jihar da tarayya, inda suka ce babu hannunsu a wannan bincike, suka kuma ce hukumar EFCC ce da ICPC, amma ba hannunsu, Namadi Sambo ya mayar da martani.

A cewar Namadi Sambo, ta hannun hadimisa, daga watan Janairu zuwa yanzu, sai shidda aka shiga bincike gidajensa, amma baá sami komai ba, wanda hakan, a cewarsa, ya nuna matsuwar gwamnatin APC kan sai lallai ta shafa masa kashin kaji domin 'á rataye shi', a siyasance.

KU KARANTA KUMA: Bamu san gaskiyar halin da lafiyar shugaba Buhari ke ciki ba - APCBamu san gaskiyar halin da lafiyar shugaba Buhari ke ciki ba - APC

Namadi Sambo ya koka kan yawan tsangwamar jami'an EFCC kan dukiyarsa

Namadi Sambo ya koka kan yawan tsangwamar jami'an EFCC kan dukiyarsa

An dai sha bincike amma baá sami komai ba, ba kuma a kama kowa ba, amma iyalan gidan na tsohon Mataimakin sunce an sha musu barnar kayan alatu dake gidan yayin binciken.

Tun dai kusan dala dubu goma da aka kama kuma aka tafi da ita daga ofishin tsohon mataimakin na Abuja, har yau babu wani babba kamu da aka yi a yakice-yakicen, sai dai a wannan karon, an zo da babbar mota mai sulke ta kudi, wadda mataimakin shugaban kasar yace, so ake a makala wasu makudan kudade ace daga gidansa aka same su.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Twitter: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel