Batun ballewar Najeriya: A fa bi hanyar lumana - Dattijo Yakubu Gowon

Batun ballewar Najeriya: A fa bi hanyar lumana - Dattijo Yakubu Gowon

- Dattijo Gowon yayi kira da matasan Najeriya da su rungumi zaman lafiya

- Kar mu yarda kasashen waje su tsoma mana hannu cikin harkokin mu na gida

- Nayi imani idan mu zauna mu tattauna mastalolin mu, zamu samu mafita

Tsohon Shugaban kasa na mulkin soji a Najeriya General Yakubu Gowon yayi kira ga kungiyar matasan Arewa da na IPOB da ke kudancin kasar da su dena ruruta wutar rigima da tashin hankali a tsakaninsu, sai dai su rungumi zaman lafiya da lumana.

A wata hira da yayi da manema labarai a garin Sokoto, General Gowon yace yayi imani yan Najeriya zasu iya warware matsalolinsu kamar yadda sukayi sulhu bayan yakin basasa a baya.

Batun ballewar Najeriya: 'A fa bi hanyar lumana' - Dattijo Yakubu Gowon

Batun ballewar Najeriya: 'A fa bi hanyar lumana' - Dattijo Yakubu Gowon

Ya cigaba da cewa babu wata kasar duniya da zata iya magance mana matsalolin mu. Ya zama dole mu dukufa wajen neman mafita tare. Tsohon shugaban ya bada misali da kasar Amurka inda yace Yan kasar sun shafe shekaru 150 bayan yakin basasar kasan kafin suka samu sassanta a tsakanin su.

KU KARANTA KUMA: Gowon ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya

Gowon ya sake nanatawa cewa duk matsalolin da Najeriya ke fama dashi yanzu za'a iya shawo kansu idan muka zauna tare a kujerar sulhu. Ya hori yan Najeriya ta kar su bari kasashen waje su tsoma musu baki cikin harkokin su na gida.

"Mu hada kanmu waje daya domin warware matsalolin da ke damun kasar mu, kar mu bari wani bare ya shigo mana cikin harkokin mu na cikin gida. Zamu iya warware matsalolin namu kamar yadda mukayi bayan yakin basasar Najeriya." Inji Gowon.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Twitter: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel