Bamu san gaskiyar halin da lafiyar shugaba Buhari ke ciki ba - APC

Bamu san gaskiyar halin da lafiyar shugaba Buhari ke ciki ba - APC

- Jam’iyyar APC ta ce bata san matsayin lafiyar shugaban kasa

- Kakakin jam’iyyar ya ce shi ba jami’in gwamnati bane

- Sannan ya ce wadanda suka sani kamar ‘yan uwansa sun sani

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa bata san halin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke ciki a yanzu ba fiye da kwanaki 50 bayan ya bar kasar don jinya.

Tafiyar shugaban kasa birnin Landan don ci gaba da jinya ya janyo martani daban-dan a kasar inda wasu da dama suka bukaci ya yi murabus.

Bolaji Abdullahi wanda ya kasance kakakin jam’iyyar APC da ya yi hira a Channels Television ya ce baida masaniya kan halin da lafiyar shugaban kasa Buhari ke ciki haka kuma jam’iyyar bata sani ba.

KU KARANTA KUMA: Gowon ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya

A lokacin wani shiri a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli ya ce: “Ban san halin da shugaban kasar ke ciki ba…haka kuma jam’iyyar (APC) bata sani ba.

Ya kuma yi magana da Premium Times inda ya tabbatar da rashin masaniyarsa a kan halin da shugaban kasar ke ciki ya kara da cewa shi ba jami’in gwamnati bane.

Ya ce: “Ni ba jami’in gwamnati bane kuma ni ba dan uwansa bane, don haka bana a cikin matsayin sani.”

“Wadanda ya kamata su sanu zasu sani.”

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta je birnin Landan don ganin shugaban kasar koda dai ana ta yada jita-jitan cewa ba’a bari ta gan shi ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel