Mutuwar Dan Masanin Kano: Gwamnatin Kano ta sanar da gobe Talata ranar hutu

Mutuwar Dan Masanin Kano: Gwamnatin Kano ta sanar da gobe Talata ranar hutu

- An bayyana gobe Talata 4 ga watan Yuli ranar Hutu

- wannan Hutu ya samu ne domin alhinin mutuwar dan masanin Kano

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Ganduje ta bayar da hutu domin jimamin rasuwar tsohon ministan mai, kuma dan Masanin Kano, Alhaji Maitama Sule.

Mataimakin gwamna Abdullahi Ganduje, akan sha’anin watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ne ya sanar da haka a ranar Litinin 3 ga watan Yuli, jim kada da sanar da mutuwar Dan Masanin.

KU KARANTA: Rikici a Masarauta: Rikita rikita a fadar Sarkin Musulmi tayi ƙamari, ta ɗauki sabon salo

Yakasai ya bayyana gwamnatin jihar ta amince da ranar Talata 4 ga watan Yuli a matsayin ranar alhinin mutuwar Dan Masani, don haka babu aiki a wannan rana, kamar yadda BBC Hausa ta samu rahoto.

Mutuwar Da Masanin Kano: Gwamnatin Kano ta sanar da gobe Talata ranar hutu

Masanin Kano

Bugu da kari an bayyana za’ayi jana’izarsa a gove Talata 4 ga watan Yuli a birnin Kano, bayan an dawo da gawarsa gida Najeriya daga kasar Masar inda yayi jinya, har zuwa cikawarsa.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito ana sa ran mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ne zai jagoranci jana’izar shahararren dan siyasan a fadar sa dake birnin Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin zaka taimaka ma Buhari don samun sauki?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel