Ka ji makudan kudin da Najeriya ta tara cikin kasa da shekaru 2

Ka ji makudan kudin da Najeriya ta tara cikin kasa da shekaru 2

– Shugaban Hukumar FIRS yace an samu karin mutane da ke biyan haraji

– Cikin shekara guda da rabi Najeriya ta samu sama da Biliyan 100

– Shugaban FIRS na kasa Fowler ya bayyana wannan a Garin Legas

Kudin da Najeriya ke samu daga haraji ya karu a halin yanzu. Wannan duk yana cikin kokarin Shugaba Fowler a wannan Gwamnati. An samu karin Mutane 400,000 da ke biyan haraji a Najeriya Inji Hukumar.

Ka ji makudan kudin da Najeriya ta tara cikin kasa da shekaru 2

Ofishin Hukumar FIRS mai tatsar kudin haraji

Shugaban Hukumar FIRS mai tatsar kudin haraji a kasa Babatunde Fowler yace kudin da Najeriya ke samu daga haraji ya karu a halin yanzu saboda tsarin da aka kawo. Fowler yace an samu karin kanfuna da mutane 400,000 da ke biyan haraji yanzu a kasar.

KU KARANTA: PDP ta nemi Shugaba Buhari yayi murabus

Ka ji makudan kudin da Najeriya ta tara cikin kasa da shekaru 2

Shugaban Hukumar FIRS Babatunde Fowler

Babatunde Fowler yace cikin shekara guda da rabi Najeriya ta samu har Naira Biliyan 118 daga haraji. Hakan dai ya yiwu ne bayan Hukumar ta hada kai da Hukumar kwastam da sauran Jami’ai.

Jam’iyyar PDP mai adawa ta nemi a zauna game da tsarin Najeriya. Yanzu haka wasu dai na nema su balle daga Najeriya inda wasu kuma ke ganin ya kamata a bar masu kasar su. Don haka ne Jam’iyyar ke gani sai an zauna.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko me ya dace ayi wa Evans mai garkuwa da mutane

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel