Ba a gayyaci Kocin Lionel Messi zuwa wajen daurin auren sa ba

Ba a gayyaci Kocin Lionel Messi zuwa wajen daurin auren sa ba

– A Ranar Juma’a ne aka auren Dan wasan Barcelona Lionel Messi

– Sai dai babban Dan wasan kasar Maradona bai halarci bikin ba

– Wannan abu ya jawo abin magana a Duniya yanzu haka

A karshen makon jiya ne Dan wasan Duniya Messi ya shiga daga ciki. Lionel Messi ya auri sahibar sa mai suna Antonella Rocuzzo a Argentina. Sai dai babban Dan kwallon kasar Diego Maradona bai je wannan daurin aure ba.

Ba a gayyaci Kocin Lionel Messi zuwa wajen daurin auren sa ba

Messi bai gayyaci tsohon Kocin sa wajen daurin auren sa ba

Rashin halartar Diego Maradona wajen bikin Dan wasa Lionel Messi ya jawo surutu ganin cewa Maradona yana cikin manyan ‘yan kwallon da aka taba yi a Duniya kuma duk kasar ake ji da shi. Kuma dai Maradona ya taba horas da Dan wasa Messi.

KU KARANTA: Babban Dan wasa Lionel Messi ya zama Ango

Ba a gayyaci Kocin Lionel Messi zuwa wajen daurin auren sa ba

Rashin Maradona wurin daurin auren Messi ya jawo magana

Ko da aka tambayi Maradona abin da ya hana a gayyace sa sai yace ba mamaki goron gayyatar ne bai iso gare sa ba har lokacin amma ya tabbatar da cewa babu wani abu da ke tsakanin sa da ’Dan wasan da yake yi wa kallon cewa kwararre ne a Duniya.

Messi ya gayyaci ‘Dan kasar sa kuma tsohon Dan wasan Real Madrid Angel Di-Maria zuwa bikin nasa da aka yi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ronaldo ya zama abokin Davido a Instagram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel