YANZU YANZU: Kakakin majalisar jihar Kano ya yi murabus kan zargin cin hanci

YANZU YANZU: Kakakin majalisar jihar Kano ya yi murabus kan zargin cin hanci

- Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya yi murabus daga majalisar dokokin jihar Kano

- Tsohon kakakin majalisar ya ce hakan zai ba da damar yin bincike kai tsaye

- An zarge shi da karban cin hanci naira miliyan 100 don rufe binciken sarki Sanusi

Alhaji Kabiru Alhassan Rurum wanda ya kasance kakakin majalisar dokoki na jihar Kano na shirin ja gefe kan bincike da ake cikin zargin aikata rashawa.

Daily Trusy ta ruwaito cewa kakakin na iya murabus a yau, Litinin, 3 ga watan Yuli kan zargin cin hanci da rashawa da akeyi a kansa.

Wata majiya ta yi ikirarin cewa Rurum ya aika wata wasika majalisa kan kudirin san a yin murabus domin a samu damar gudanar da bincike yadda ya dace.

KU KARANTA KUMA: Matasa sun ba shugaba Buhari wa’adin makonni 8 ya yi murabus

Anyi zargin cewa kakakin ya karbi kimanin naira miliyan 100 daga Alhaji Aliko Dangote domin a dakatar da bincike da kuma tsige sarkin Kano, Malam Muhgammadu Sanusi.

An rahoto cewa majalisar zata zauna don tattaunawa a kan wasikar da kakakin ya aika.

Sabon kakakin majalisar da aka rantsar bayan murabus din Yusuf Abdullahi Attah ya sha alwashin ci gaba da mu’ammala da dan majalisar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com da sarki Sanusi ke magana a kan tsarin shugabancin Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel